Hukumar JAMB ta shirya taro kan bai wa naƙasassu dama
Manage episode 441562285 series 1083810
Shirin namu na wannan mako zai yi dubi ne kan yadda hukumar kula da harkar jarabawan shiga jami’o’i a Najeriya wato JAMB da hadin guiwan kungiyar zabiya na kasa ta shirya taron nahiyar Afrika na farko kan baiwa nakasassu ko masu larura ta musamman dangane da harkar ilimi kamar kowani dan adam.
Taron an shirya shi ne dai la’akari da irin kalubalen da masu larura ta musamman ke fama da ita a kasashe masu tasowa kamar Najeriya,kama daga kyama,nuna musu banbanci da dai sauransu.
23 эпизодов